‘Bikin zagayowar ranar dimokradiyya ba shi da amfani a Najeriya’

By | May 28, 2018

44 total views, 3 views today

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta ce ba bu wani amfani da bikin zagayowar dimokradiyya zai yi wa ‘yan kasar.

Loading...

A cikin wata sanarwa da ta fitar, PDP, ta ce, babu wani abu da ‘yan Najeriya ke gani a cikin wannan mulki bayan take hakin dan adam.

Mataimaki na musamman a jam’iyar ta PDP a bangaren watsa labarai a yankin arewacin Najeriya, Shehu Yussuf Kura, ya shaida wa BBC cewa, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba ta dauki wani mataki na habaka dimokradiyya ba a kasar, illa ma takura shi da yi masa zagon kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Loading...