Buhari bai iya mulki ba-Shekarau

By | May 15, 2018

30 total views, 3 views today

Tsohon Gwmanan jihar Kano ya ce zai sauya fasalin yadda ake gudanar da mulki idan ya zama shugaban kasar

Malam Ibrahim Shekarau ya ce zai sauya fasalin yadda ake gudanar da mulki idan ya zama shugaban kasar
Image caption Malam Ibrahim Shekarau ya ce zai sauya fasalin yadda ake gudanar da mulki idan ya zama shugaban kasar

A Najeriya,Tsohon gwamnan Kano Mallam Ibrahim Shekarau, ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari bata tabuka wani abun azo a gani a tsawon fiye da shekaru uku da ta yi kan mulkin kasar.

A wata hira da BBC Malam Ibrahim Shekarau ya ce yadda gwamnatin Buharina tafiyar da mulki tamkar bata san abun da take ba.

Shi dai Shugaba Muhammadu Buhari yana fuskantar zazzafan kalubale yayin da zaben 2019 ke kara karatowa.

Loading...

Tsohon Gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar PDP ya ce zai sauya fasalin yadda ake gudanar da mulki idan ya zama shugaban kasar.

Ya kuma musanta zarge zargen cewa yana da hannu a rarraba kudaden da ake zargin an wawure gabannin zaben 2015.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Loading...