Karanta abubuwan da ‘ke sa mutum ya dade a duniya’

By | May 18, 2018

23 total views, 3 views today

illustration for life expectancy

Mata sun fi maza dadewa a duniya a kasashe 195, kuma a Rasha sun fi su da shekara 11.

‘Yan kasar Ethiopia suna fin wadanda suka yi rayuwa a shekaraun 1990 da shekara 19, kuma mutanen da suke kasashen da suka ci gaba sun fi mutanen da suka fi karancin shekaru a shekarun 1990 da shekara 34.

Wannan kadan ne daga cikin abubuwan da BBC ta gano ta kalkuletar shekarun da ake hasashen mutum zai yi a duniya, wadda ta yi amfani da alkaluma daga binciken tasirin cututtuka ko Global Burden of Disease Project, wadda cibiyar da ke nazari a kan lafiya ta IHME ta gudanar.

Ga abubuwan da aka gano a nan.

1.Tsawon rayuwarmu na karuwa

Tsawon rayuwar mutane a duniya ya karu da sama da shekaru bakwai tun shekarun 1990, wanda ke daidai da samun karin shekara cikin ko wacce shekara uku da rabi.

Mutane daga sassan duniya suna kara tsawon rayuwa saboda raguwar mutuwa kan cututtukan zuciya a kasashen da aka fi samun kudaden shiga, da kuma raguwar mutuwar yara a kasashen da aka fi karancin kudaden shiga.

Ingantancen shirin kiwon lafiya da tsaftace muhalli da kuma cigaba wajen maganin cututtuka sun bayar da gudumawa wajen kara tsawon rayuwar.

Tsawon rayuwa mai lafiya – adadin shekarun da za ka iya yi kana cikin koshin lafiya – shi ma ya karu da shekara 6.3. Sai dai kuma, iya adadin karuwar tsawon lokacin na duniya kuma ya fara raguwa.

2. Kasashen Yammacin Turai sun fi yawa a sama

Goma sha hudu daga cikin kasashe 20 masu yawan tsawon rayuwa suna Turai ne, sai dai kuma yankin Asiya ta Gabas tana gaban kowa: mutanen da aka haifa a yau a Japan da Singapore za su iya sa ran kai wa shekara 84 a duniya.

Game da kasashen Birtaniya kuwa, Ingila ta shiga cikin kasashe 20 da ke kan gaba da tsawon rayuwa da ya kai shekara 81, yayin da yankin Arewa na Ireland yana ta 32, shi kuma da yankin Wales ke na 34, dukkansu da shekara 80.

Scotland ce ta 42 cikin kasashe 198 da tsawon rayuwa na shekara 79.

3. Kasashen Afrika ne suka fi yawa a kasa

Dukkan kasashe 20 din da ke kasa, in ban da guda biyu, daga Afirka suke.

Yaran da aka haifa a shekarar 2016 a Lesotho Jamhuriyar Tsakiyar Afrika – wadda yakin basasa ya daidaita – suna da tsawon rayuwa na shekara 50, suna kasa da na ‘yan Japan da shekara 34.

Shekarun da aka shafe ana yaki da kuma rashin doka a Afghanistan, wadda ita ce kasar Asiya daya tilo da take kusa da kasa, sun sa tsawon shekaru a kasar yana kan 58.

4. Mata sun fi dadewa a duniya

Mata sun fi maza a kasashe 195 cikin kasashe 198, inda suke fin su da kimanin shekara shida.

Duk da haka, a wasu kasashe wannan ratar ta kai shekara 11.

Kamar yadda taswirar da ke kasan nan ta nuna, mafi yawan ratar da ake samu tsakanin maza da mata suna kasashen gabashin Turai ne da Rasha, inda aka yi bayanin cewar shan barasa da kuma rashin wurin aiki mai kyau ke rage tsawon rayuwar maza.

Loading...

Kasashen uku da maza suka fi mata dadewa a duniya su ne Jamhuriyar Congo da Kuwait da kuma Mauritaniya.

5. A kasar Habasha, tsawon rayuwa ya karu da shekara 19

Tun shekarar 1990, tsawon rayuwa ya inganta a kashi 96 cikin dari na kasashen duniya.

A wancan lokacin, ba a tsammanin mutanen da aka haifa a kasashe 11 su wuce shekara 50 ba, duk da haka ko wacce kasa ta kai ga wannan muhimmin matakin a shekarar 2016.

Shida daga cikin wadannan kasashen da aka samu samu wannan cigaban suna yankin kudu da hamadar Afirka ne.

Kasar Habasha da har shekarar 1990 ke farfadowa daga fari tana da tsawon rayuwa da ya kai shewkara 47.

Za a iya tsammanin ‘ya’yan da aka haifa a wurin a shekarar 2016 su dara na da da shekara 19 saboda muhimmin raguwar da aka samu a cututtukar numfashi da kuma gudawa kamar cutar kwalera.

6. Sai dai kuma, tsawon rayuwa ya fadi a kasashe takwas

Duk da cewar tana cikin yankunan da suka fi samun yawan tsawon rayuwa, yankin Afirka na kudu da Sahara yana da kasashe hudu da cikin kasashe takwas din da tsawon rayuwa ya ragu tun shekarun 1990.

A Lesotho ne a ka samu raguwar tsawon rayuwa mai yawa, a inda bisa kiyasin Majalisar Dinkin Duniya, ko wane daya daga cikin mutum hudu ke da cutar HIV – wuri na biyu da aka fi yawan matsalar a duniya.

Yaran da aka haifa a Afirka ta Kudu a shekarar 2016 za su iya tsammani su rayu zuwa shekara 62 – shekara biyu kasa da takwarorinsu da aka haifa a shekara 25 da ya wuce cikin shekarar 1990. A wannan lokacin, kasar ta yi fama da tasirin annobar HIV.

7. Bambance-bambancen da suka dara kan iyaka

Tsawon rayuwa ka iya zama abun da ya kebanta a wuri daya – wasu kasashen makwabta suna da kusan shekara 20 tsakaninsu.

Alal misali, idan aka tsallake daga China zuwa Afghanistan, tsawon rayuwa zai fadi da sama da shekara 18.

Kuma kasar Mali – wadda ta shafe shekaru tana fama da ta’addanci da kuma tashe-tashen hankula a cikin ‘yan shekaru goman nan – tana da tsawon shekara 62 ne kawai, amma mutanen da aka haifa a kasar Aljeriya mai makwabtaka za su iya fatan kaiwa shekara 77a duniya.

8. Yaki na da mummunar tasiri

A shekarar 2010, an saka Syria a matsayin kasa ta 65 a duniya a fagen tsawon rayuwa, cikin kashi daya cikin uku na kasashe, wadanda suke kan gaba.

Sai dai kuma shekarun da aka shafe ana yake-yake sun sa kasar ta koma ta 142 a shekarar 2016.

A lokacin da ake kan kisan kiyashin Rwanda a shekarar 1994, tsawon rayuwa bai wuce shekara 11 ba.

9. Kamar yadda fari da bala’i ke yi

Koriya ta Arewa ta fuskanci fari mai matukar muni tsakanin shekarar 1994 da kuma shekarar 1998 wanda ya rage tsawon rayuwar mutanenta da shekaru har zuwa farkon shekarun 2000.

Sama da mutane 200,000 aka kiyatsa cewa sun mutu girgizar kasar da aka yi a Haiti a shekarar 2010. Sai dai kuma tsawon rayuwa ya sake karuwa a shekarar 2001.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Loading...