Tsohon jagoran ‘yan shi’a Moqtada al-Sadr na gab da lashe zaben Iraqi

By | May 15, 2018

23 total views, 3 views today

Wasu magoya bayan Moqtada al-SadrHakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tun ranar litinni magoya bayan Moqtada al-Sadr ke bikin nasara a birnin Bagadaza

Hadakar da tsohon shugaban mayakan shi’a ke jagoranta a Iraqi, Moqtada al-Sadr, na kan hanyar lashe zaben kasar da aka gudanar a karshan mako, bayan sanar da sama da kashi 90 na kuri’un da aka kada.

Mista Sadr dai bai tsaya takarar Firaminista ba, sai dai nasarar mamaki da hadakarsa za ta samu zai bashi daman tasiri wajen zaben wanda zai samu wannan mukami.

Wakilin BBC ya ce wannan babban nasara ce ga Moqtada al-sadr, wanda ya bayyana kansa a matsayin fitacce da ke adawa da rashawa, kuma ya yi fice wajen nuna adawa ga Amurka da kuma Iran.

Loading...

Firai ministan mai-ci Haider Abadi, ya gaza kai wa abinda aka yi tsanmani, duk da nasarar da Iraqi ta yi a kan kungiyar IS a karkashinsa.

Al-Abadi ya bukaci dukkanin jam’iyyun siyasar kasar da su mutunta sakamakon zaben.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Loading...