Yadda gwaggon biri ya kai wa ‘yar shekara daya hari a Zimbabwe

By | May 15, 2018

32 total views, 3 views today

BiriHakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan al’amari dai sh ne na baya-baya kan irin rikicin da ake samu tsakanin mutane da birrai a Chinotimba da ke kusa da koramar Victoria

Wata uwa a zimbabwe ta bayar da labarin tashin hankalin da ta shiga a yayin da wani gwaggon biri ya kafa hakoransa a fuskar ‘yarta a harabar gidansu.

Matar mai suna Jean Gama ta shaida wa kafar watsa labarai ta Bulawayo24 cewa ala tilas ta rufe birin da duka da wani rodi don ta tursasa shi ya sake mata ‘yar tata mai shekara daya, wacce ta galabaita kuma jini yake ta fita a jikinta.

Wannan al’amari dai shi ne na baya-baya kan irin rikicin da ake samu tsakanin mutane da birrai a Chinotimba da ke kusa da koramar Victoria.

A takaice dai Ms Goma ta ce, a lokacin da suka isa asibiti, ta ga wani mutum da shi ma birin ya ciza yana jira a yi masa magani.

An yi amannar cewa birin ya kai wa yarinyar hari ne, wacce ke wasa a waje tare da yayanta, saboda birin ya so ya kwace ‘yar tsanar yarinyar.

Loading...

Reuben Dube, wanda ke zaune a yankin, ya ce a yanzu iyaye kan raka ‘ya’yansu zuwa makaranta saboda irin yadda dabbobi ke tunkarar su.

Ya shaida wa Bulawayo24 cewa: “Mun yi ta kai korafi ga Hukumar Kula da Gandun Daji ta Zimbabwe wato (Zimparks), amma har yanzu ba su yi komai a kai ba.”

Wani mai magana da yawun ZimParks ya ce hakkin mazauna yankin ne su kare kansu daga hadarin da suke fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Loading...